Bayanin Mene ne Ihrami
Ma'anar Ihrami A Larabci
Shi ne : Hanawa ko Kariya
Ma'anar Ihrami A Shari'a
Shi ne niyyar shiga aikin hajji, tare da wani abu na ayyukan hajji
Abubuwan Da Ake So Mai Ihrami Ya Yi
1 – Wanka
An karvo daga Kharijah xan Zaid, daga babansa, ya ce, “shi ya ga Annabi
(SAW) ya cire kayansa ya yi wanka saboda ihrami” [Tirmizi ne ya rawaito
shi]
2 – Tsaftace Jiki
Ta hanyar cire gashin hammata da mara, da yanke gashin baki da farce
3 – Turare
Saboda hadisin Aisha – Allah ya yarda da shi – “Na kasance
ina sa wa Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) turare, saboda zai sanya ihraminsa”
[Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi].
Amma kada ya sanya wa kayansa turare, saboda faxin Manzon
Allah ( صلى الله عليه وسلم ) “Kada ku sanya kayan da turaren Za'afaranu
ya shafe su, ko kuma turaren wars”[Bukhari da Muslim
ne suka rawaito shi].
Turare
2 – Sanya xinkakken Abu ga Maza
Abin da ake nufi da xinkakke shi ne duk abin da aka xinka
shi don sa wa a wata gava ko a jiki, kamar riga, wanduna, huffi,
safa, safar hannu da makamantansu, saboda hadisin Xan Umar da
ya gabata : “ Kada ku sanya riguna, ko rawuna, ko wanduna,
ko kuma rigunan da suke haxe da hula, ko huffi”[Bukhari
da Muslim ne suka rawaito shi]
Idan mai ihrami bai samu kwarjalle ba to zai iya sanya
wando har zuwa lokacin da zai samu kwarjalle, haka nan idan
ban samu takalma faxe ba, to ya sanya huffi, saboda faxin
Annabi ( صلى الله عليه وسلم )
“ Idan bai samu takalmi faxe ba, to ya sanya huffi, amma
ya yanke su zuwa idon sau”[Ibnu Khuzaima ne ya rawaito
shi]
Sanya
Xinkakken Abu
Takalma
Guda Biyu
Riga
Mai Haxe Da Hula
Huffin
Mai Ihrami
3 – Kashe dabbar tudu ko farautarta
Saboda faxin Allah Maxaukakin Sarki : “Kada ku kashe
dabbar farauta alhali kuna cikin ihrami” (Al-ma’idah
: 95).
Ma’ana kun yi haramar aikin hajji ko umara. Hakanan da faxin
Allah Maxaukakin Sarki : “An haramta muku farautar dabbobin
tudu matuqar kuna cikin ihrami”. (Al-ma’idah
: 96)
abin da ake nufi dabbar da take jeji wadda ba a saba da ita
ba, hakanan ma tsuntsaye.
Amma dabbobin da aka saba da su, waxannan ba farauta ba ne.
Ya halatta mai ihrami ya yanka kamar irin su kaza, ko wata dabbar
gida da makamantansu.
Dabbobin da suke cikin ruwa ma ya halatta
mai ihrami ya yi farautarsu.
Saboda faxin Allah Maxaukakin Sarki : “An halatta
muku farautar dabbobin ruwa da mushensa (dabbar da mutu a cikin
ruwa wadda take rayuwa a ciki” (Al-ma’idah :
96).
Amma dabbobin da aka haramta cin su kamar maciji, kunama,
ya hallata a kashe su, kuma ya halatta mai ihrami ya kashe duk
wata dabba da ta taso masa, idan ba zai iya ture ta ba sai da
hakan.
Kunama
Maciji
Ya
Halatta A Yanka Dabbar Gida
Tsuntsayen
Da Ake Farauta
Su ya
halatta ga mai ihrami
4 – Aski Ko Saisaye
Saboda faxin Allah Maxaukakin Sarki : “Kada ku aske
kawunanku har sai dabbar hadaya ta isa mahallinta”.
(Al-baqara : 197).
Wannan hanin ya haxa dukkan jiki gabaxayansa, idan aka yi
qiyasi da gashin kai.
Aski
Ko Saisaye
5 – Yanke Farce
Farcen qafa ne ko na hannu.
Yanke
Farcen Qafa
Yanke
farcen Hannu
6 – Sanya Turare A Jiki Ko Kaya
An hana mai ihrami ya sanya turare a jikinsa ko tufafinsa
bayan ya shiga ihrami, ko kuma ya shaqi turare, saboda hadisin
xan Umar – Allah ya yarda da shi – wanda ya gabata, a cikinsa
Manzon Allah ya ce, “Kada ku sanya kayan da turaren Za’afaranu
ya shafe su, ko kuma turaren wars”[Bukhari da Muslim
ne suka rawaito shi]
Da hadisin mutumin nan da ya mutu yana cikin ihrami, Manzon
Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya ce, “Kada ku sanya masa turare”[Bukhari
ne ya rawaito shi]
Sanya
wa Jiki Turare
Sanya
wa Riga Turare
7 – Xaura Aure
Saboda hadisin Usman – Allah ya yarda da shi – ya ce, Manzon
Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya ce, “Mai ihrami baya aura, ba a aurar masa,
baya neman aure”[Muslim ne ya rawaito shi].
8 – Saduwa Da Mace
Shi ne tarawa da mace, saboda faxin Allah Maxaukakin Sarki
: “Duk wanda ya shiga aikin hajji a cikinsu to babu
saduwa da mata”. (Al-baqara : 197)
Abdullahi xan Abbas – Allah ya yarda da shi – ya ce, “Ana
nufin jima’i” kuma shi ne mafi tsananin abin da aka hana mai
ihrami
9 – Rungumar Mace Ba Tare Da Saduwa ba
Kamar sumba da shafa, saboda hanya ce ta zuwa saduwa.
Abubuwan Da Aka Haramta Wa Mace Mai Ihrami
Mace a wajen abin da aka hana mai ihrami kamar namiji
ce, sai dai ta bambanta da shi ne a abubuwa masu zuwa :
1 – Zata sanya xinkakken kaya.
2 – Zata rufe kanta.
3 – Ba za ta rufe fuskarta ba (Niqab), ba za ta sanya
safa ba, saboda faxin Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم
) : “Mace mai
ihrami ba za ta rufe fuskarta ba, (niqab) ba za sanya safar
hannu ba”[Bukhari ne ya rawaito shi]
Amma za ta rufe fuskarta a wajen mazajen da ba na ta
ba, ta hanyar sakin mayafinta, ba niqabi zata sanya ba,
kuma an halatta mata yin ado da zinare.
Faxakarwa
1 – Abin da ake kira raka’a biyu bayan Ihrami bai da asali,
kamar yadda babu wata addu’a da aka ayyana yayin Ihrami.
2 – Idan mutum yana tafiya a jirgi, kuma ya ji tsoron
ba zai samu damar sanya Ihrami ba idan ya isa miqati, to
ya sanya ihramin daga gidansa ko filin jirgin sama, amma
bai zama mai ihrami ba har sai ya yi niyyar aikin hajji
kafin ya wuce miqati.
3 – Wasu alhazai suna yaye kafaxunsu da zarar sun sanya
ihraminsu, abin da ake kira da larabci «Alix-xiba’i».
To yin hakan ba daidai ba ne, saboda ana yaye kafaxu
a buxe a wurin xawafi kaxai, a sauran wurare kuwa sai alhaji
ya rufe kafaxunsa.
Fito Da Kafaxa Waje Yayin Ihrami
Wasu Daga Hukunce-Hukuncen Ihrami :
Idan gashi ya faxi da kan mai ihrami saboda ya shafar
kansa yayin alwala ko wanka, to wannan ba zai cutar da shi
ba, haka nan idan gashin bakinsa ya cire ko na gemunsa ko
farcensa, babu komai, matuqar ba da gangan ya cire shi ba.
Mace da namiji duk hukuncinsu xaya, saboda mace ma idan
gashinta ko farcenta ya cire babu komai a kanta.
Ya halatta mai ihrami ya sanya maxauri a qafarsa idan
yana buqatar hakan, ko kuma saboda wata maslaha.
-Sanya Sharaxi Yayin Niyya :
Wanda yake da rashin lafiya, ko ya ji tsoron faruwar
wani abu da zai hana shi gama aikin hajjinsa, to an so ya
yi sharaxi yayin sanya ihrami, ya ce, «Allah na amsa maka
da umara ko hajji, amma idan wani abu ya tsare ni, to wurin
cire ihrami na shi ne inda aka tsare ni».
An karvo daga Aisha – Allah ya yarda da ita – ta ce,
“Manzon Allah (SAW) ya shigo wajen Duba’a ‘yar Zubair,
ya ce mata, “Ko zaki je aikin hajji ne?” sai ta ce, “Wallahi
ina ji na bani da lafiya” sai Manzon Allah (SAW) ya ce mata,
“Ki tafi hajji, ki sanya sharaxi, ki ce, “Ya Ubangiji wurin
cire ihramina shi ne wurin da aka tsareni (Wato wurin rashin
lafiya ta taso min) idan kin faxi haka, kuma wani abun da
zai hana ki ya faru, to ya halatta ki fita da ihraminki,
babu wani abu a kanki”[Bukhari da Muslim ne suka
rawaito shi]