facebookgoogle plustwitteryoutube
Bitar Abin Da Ya Gabata (Ka San Allah Wanda Babu Abin Bautawa Da Gaskiya Sai Shi)-2
638

Bitar Abin Da Ya Gabata (Ka San Allah Wanda Babu Abin Bautawa Da Gaskiya Sai Shi)-2

1-Mene ne so?

2-Faxin tasirin sonka ga Allah a rayuwarka?

3-Shin zai yiwa a bautawa Allah da so kawai, ba tare da tsoro ko fata ba? Kafa hujja akan abin da kake faxa da halin Annabawa?

4-Me zai faru ga bawa idan Allah ya so shi?

5-Bayyana alaqar abin da ka sani na sunayen Allah da siffofinsa da son shi.

6-Shin fata a wajen Allah yana sa a yi aiki? Yi bayanina kan haka, a bisa hasken faxin Allah Maxaukakin Sarki “Duk wanda yake fatan gamuwa da Ubangijinsa to ya yi aiki na qwarai kada ya haxa Allah da wani a wajen bauta” (Alkahfi : 110)

7-Shin fata a wurin Allah yana nufin rashin tsoronsa? Ko kuwa tsoron Allah yana lazimtar rashin fata gare shi?

8-Faxi abin da ka sani na sunayen Allah da soffofinsa waxanda suke wajabta fata a gare shi?

9-Lissafo abubuwan da suke qara maka tsoron Allah?

10-Faxi abin da ka sani na sunayen Allah da sifofinsa waxanda suke kawo tsoron Allah.

11-Me ye ya dace da wanda yake jin tsoron Allah ya aikata?

12-Mene ne mafi qarancin tasirin da ake samu na ayyukan ibada, irin sallah da zakka, da azumi da hajji, a halayar musulmi?

13-Ta yaya za a suranta Imanin wanda ba ya sallah? Faxi dalili akan abin da kake faxa.

14-Zai yi wu a ce mutum yana sallah, kuma sallarsa ba ta hana shi alfasha da abin qi ba?

5-Ta yaya alaqar imani da Allah da kuma mu’amala da mata, da ‘ya’ya da yan uwa, da maqota da mutane gabaxaya take bayyana?