Surah [ Aal-imraan ] ayah [130] Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Kada ku ci riba ninkininki, riɓanye, kuma ku bi Allah da taƙawa, tsammãninku zã ku ci nasara.
Surah [ Gafir ] ayah [39] "Kuma ya mutãnħna! Wannan rãyuwa ta dũniya dan jin dãɗi ne kawai, kuma lalle Lãhira ita ce gidan tabbata."
Surah [ Al-baqara ] ayah [281] Kuma ku ji tsõron wani yini wanda ake mayar da ku a cikinsa zuwa ga Allah, sa´an nan kuma a cika wa kõwane rai abin da ya sanã´anta, kuma sũ bã a zãluntar su.
Surah [ Al-fath ] ayah [29] Muhammadu Manron Allah ne. Kuma waɗannan da ke tãre da shi mãsu tsanani ne a kan kãfirai, mãsu rahama ne a tsakãninsu, kanã ganin su sunã mãsu rukũ´i mãsu sujada, sunã nħman falala daga Ubangijinsu, da yardarSa. Alãmarsu tanã a cikin fuskõkinsu, daga kufan sujuda. Wannan shĩ ne siffarsu a cikin Attaura. Kuma siffarsu,a cikin Injĩla ita ce kamar tsiron shũka wanda ya fitar da rħshensa, sa´an nan ya ƙarfafa shi, ya yi kauri, sa´an nan ya daidaita a kan ƙafãfunsa, yanã bãyar da sha´awa ga mãsu shũkar´ dõmin (Allah) Ya fusãtar da kãfirai game da su. Kuma Allah Ya yi wa´adi ga waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, daga cikinsu, da gãfara da ijãra mai girma.
Surah [ xaha ] ayah [132] Kuma ka umurci iyãlanka da salla, kuma ka yi haƙuri a kanta. Bã Mu tambayar ka wani arziki Mu ne Muke azurta ka. Kuma ãƙiba mai kyau tanã ga taƙawa.