islamkingdomfaceBook islamkingdomtwitter islamkingdomyoutube islamkingdomnew


Kuma ´yan Aljanna suka kirãyi ´yan Wuta suka ce: "Lalle ne mun sãmi abin da Ubangijinmu Ya yi mana wa´adi, gaskiya ne. To, shin, kun sãmi abin da Ubangijinku Ya yi muku wa´adi, gaskiya?" Suka ce: "Na´am." Sai mai sanarwa ya yi yħkuwa, cħwa: "La´anar Allah ta tabbata a kan azzãlumai."

"Waɗanda suke kangħwa daga hanyar Allah, kuma sunã nħman ta ta zama karkatacciya,. kuma sũ, game da Lãhira, kãfirai ne."

Kuma a tsakãninsu akwai wani shãmaki, kuma a kan A´arãf akwai wasu maza sunã sanin kõwa da alãmarsu; Kuma suka kirãyi abõkan Aljanna cħwa: "Aminci ya tabbata a kanku: "Ba su shige ta ba, alhãli kuwa sũ, sunã tsammãni.

Kuma idan an jũyar da gannansu wajen abõkan wuta, su ce: "Yã Ubangijinmu! Kada Ka sanyã mu tãre da mutãne azzãlumai."

Kuma abõkan A´araf suka kirãyi wasu maza, sunã sanin su da alãmarsu, suka ce: "Tãrawar dũkiyarku da abin da kuka kasance kunã yi na girman kai, bai wadãtar ba daga barinku?"

"Shin, waɗannan ne waɗanda kuka yi rantsuwa, Allah bã zai sãme su da rahama ba? Ku shiga Aljanna, bãbu tsõro a kanku, kuma ba ku zama kunã baƙin ciki ba."

Kuma ´yan wuta suka kirãyi ´yan Aljanna cħwa: "Ku zubo a kanmu daga ruwa kõ kuwa daga abin da Allah Ya azurta ku." Su ce: "Lalle ne Allah Ya haramtã su a kan kãfirai."

"Waɗanda suka riƙi addininsu abin shagala da wãsa, kuma rãyuwar dũniya ta rũɗe su." To, a yau Munã mantãwa da su, kamar yadda suka manta da haɗuwa da yininsu wannan, da kuma abin da suka kasance da ãyoyinMu sunã musu.