islamkingdomfaceBook islamkingdomtwitter islamkingdomyoutube islamkingdomnew


Kuma suka ce: "Ku kasance Yahũdãwa ko Nasãra, kwã shiryu."Ka ce: "A´a aƙidar Ibrãhĩm dai, maikarkata, zuwa ga gaskiya, kuma bai kasance daga mãsu shirki ba."

Ku ce: "Mun yi ĩmãni da Allah, da abin da aka saukar zuwa gare mu, da abin da aka saukar zuwa ga Ibrãhĩm da Ismã´ĩla da Is´hãka da Ya´aƙũbu da jĩkõki, da abin da aka bai wa Mũsã da Ĩsã, da abin da aka bai wa annabãwa daga Ubangijinsu, bã mu rarrabħwa a tsakãnin kõwa daga gare su, kuma mu, a gare Shi, mãsu miƙa wuya ne."

To, idan sun yi ĩmãni da misãlin abin da kuka yi ĩmãni da shi, to, lalle ne sun shiryu, kuma idan sun jũya bãya, to, suna a cikin sãɓãni kawai sabõda haka Allah zai isar maka a gare su, kuma Shi ne Mai ji, Masani.

Rinin Allah! Kuma wãne ne mafi kyau ga rini daga Allah? Kuma mu, a gare Shi, mãsu bautãwa ne.

Ka ce: Shin kuna jãyayyar hujia ne da mu a cikin al´amarin Allah, alhãli kuwa Shi ne Ubangijinmu kuma Ubangijinku, kuma muna da ayyukanmu, kuma kuna da ayyukanku, kuma mũ, a gare Shi, mãsu tsarkakħwane?

Ko kuna cħwa: Lalle ne, Ibrãhĩm da Ismã´ĩla da Is´hãƙa da Ya´aƙũbu da Jĩkõki, sun kasance Yahũdãwa kõ kuwa Nasãra? Ka ce: Shin kũ ne kuke mafi sani kõAllah? Kuma wãne ne ya zama mafi zãlunci daga wanda ya bõye shaida a wurinsa daga Allah? Kuma Allah bai zama Mai gafala ba daga abin da kuke aikatãwa!

Waccan, wata al´umma ce, tã riga ta shige, suna da abin da suka sana´anta kuma kuna da abin da kuka sana´anta kuma bã a tambayar ku daga abin da suka kasance suna aikatãwa.