islamkingdomfaceBook islamkingdomtwitter islamkingdomyoutube islamkingdomnew


Kada ku ce ga waɗanda ake kashħwa a cikin hanyar Allah: "Matattu ne." ôa, rãyayyu ne, kuma amma bã ku sansancħwa.

Kuma lalle ne, Muna jarrabar ku da wani abu daga tsõro da yunwa da naƙasa daga dũkiya da rãyuka da ´ya´yan itãce. Kuma ka yi bishãra ga mãsu haƙuri.

Waɗanda suke idan wata masĩfa ta sãme su, sai su ce: "Lalle ne mũ ga Allah muke, kuma lalle ne mũ, zuwa gare Shi, muke kõmãwa."

Waɗannan akwai albarku a kansu daga Ubangijinsu da wata rahama. Kuma waɗannan sũ ne shiryayyu.

Lalle ne Safã da Marwa suna daga wurãren ibãdar Allah, to, wanda ya yi hajin Ɗãki kõ kuwa ya yi Umra, to, bãbu laifi a kansa ga ya yi ɗawãfi gare su, su biyu. Kuma wanda ya ƙãra yin wani aikin alhħri to, lalle ne Allah Mai gõdiya ne, Masani.

Lalle ne waɗanda suke ɓõyħwar abin da Allah Ya saukar da ga hujjõji bayyanannu, da shiriya, daga bãyan Mun bayyana shi ga mutãne, a cikin Littãfi (Alƙur´ãni), waɗannan Allah Yana la´anar su, kuma mãsu la´ana suna la´anar su.

Sai waɗanda suka tũba,kuma suka gyãra, kuma suka bayyana, to waɗannan Ina karɓar tũba a kansu kuma Nĩ ne Mai karɓar tũba, Mai jin ƙai.

Lalle ne, waɗanda suka kãfirta kuma suka mutu alhãli kuwa suna kãfirai, waɗannan akwai, a kansu, la´anar Allah da Malã´iku da mutãne gabã ɗaya.

Suna madawwama a cikinta, bã a sauƙaƙa azãba daga barinsu, kuma ba su zama ana jinkirta musu ba.

Kuma Ubangijinku Ubangiji Guda ne. Bãbu wani Ubangiji fãce Shi, Mai rahama, Mai jin ƙai.