islamkingdomfaceBook islamkingdomtwitter islamkingdomyoutube islamkingdomnew


Misãlinsu shĩ ne kamar misãlin wanda ya hũra wuta, to, a lõkacin da ta haskake abin da yake għfensa (na abin tsõro), Allah Ya tafi da haskensu, kuma Ya bar su a cikin duffai, bã su gani.

Kurãme, bħbãye, makãfi, sabõda haka bã su kõmõwa.

Ko kuwa kamar girgije mai zuba daga sama, a cikinsa akwai duffai da tsãwa da walƙiya: suna sanyãwar yãtsunsu a cikin kunnuwansu dãga tsãwarwakin, dõmin tsõron mutuwa. Kuma Allah Mai kħwayewa ne gã kãfirai!

Walƙiyar tana yin kusa ta fizge gannansu, ko da yaushe ta haskakã musu, sai su yi tafiya a cikinta, kuma idan ta yi duhu a kansu, sai su yi tsaye. Kuma dã Allah Yã so, sai Ya tafi da jinsu da gannansu. Lalle ne Allah a kan dukan kõme Mai ĩkon yi ne.

Yã ku mutãne! Ku bauta wa Ubangjinku, Wanda Ya halicce ku, kũ da waɗanda suke daga gabãninku, tsammãninku ku kãre kanku !

Wanda Ya sanya muku ƙasa shimfiɗa, kuma sama gini, kuma Ya saukar da ruwa daga sama, sa´an nan Ya fitar da abinci daga ´ya´yan itãce game da shi, sabõda ku. Sabõda haka kada ku sanya wa Allah wasu kĩshiyõyi, alhãli kuwa kuna sane.

Kuma idan kun kasance a cikin shakka daga abin da Muka sassaukar ga Bãwanmu, to, ku zõ da sũra guda daga misalinsa (Alƙur´ãni). Kuma ku kirãwo shaidunku baicin Allah, idan kun kasance mãsu gaskiya.

To, idan ba ku aikata (kãwo sura) ba, to, bã zã ku aikata ba, sabõda haka, ku ji tsoron wuta, wadda makãmashinta mutãne da duwãtsu ne, an yi tattalinta dõmin kãfirai.