islamkingdomfaceBook islamkingdomtwitter islamkingdomyoutube islamkingdomnew


Yã Mutãnen Littãfi! Don me kuke lulluɓe gaskiya da ƙarya, kuma kuke ɓõye gaskiya, alhãli kuwa kuna sane?

Kuma wata ƙungiya daga Mutãnen Littãfi ta ce: "Ku yi ĩmãni da abin da aka saukar a kan waɗanda suka yi ĩmãni (da Muhammadu) a farkon yini, kuma ku kãfirta a ƙarshensa; tsammãninsu, zã su kõmõ."

"Kada ku yi ĩmãni fãce da wanda ya bi addininku." Ka ce: "Lalle ne, shiriya ita ce shiriyar Allah. (Kuma kada ku yi ĩmãni) cħwa an bai wa wani irin abin da aka bã ku, kõ kuwa su yi musu da ku a wurin Ubangijinku." Ka ce: "Lalle ne falala ga hannun Allah take, yana bãyar da ita ga wanda Yake so, kuma Allah Mawadãci ne, Masani."

Yanã keɓance wanda Ya so da rahamarSa, kuma Allah Ma´abucin falala ne, Mai girma.

Kuma daga Mutãnen Littãfi akwai wanda yake idan ka bã shi amãnar kinɗãri , zai bãyar da shi gare ka, kuma daga gare su akwai wanda idan ka bã shi amãnar dĩnari, bã zai bãyar da shi gare ka ba, fãce idan kã dawwama a kansa kanã tsaye. Wannan kuwa, dõmin lalle ne sũ sun ce, "Bãbu laifi a kanmu a cikin Ummiyyai." Suna faɗar ƙarya ga Allah, alhãli kuwa suna sane.

Na´am! Wanda ya cika alkawarinsa, kuma ya yi taƙawa, to, lalle ne Allah yana son mãsu taƙawa.

Lalle ne waɗanda suke sayen ´yan tamani kaɗan da alkawarin Allah da rantsuwõyinsu, waɗannan bãbu wani rabo a gare su a Lãhira, Kuma Allah bã Ya yin magana da su, kuma bã Ya dũbi zuwa gare su, a Rãnar Ƙiyãma, kuma bã Ya tsarkake su, kuma sunã da azãba mai raɗaɗi.