islamkingdomfaceBook islamkingdomtwitter islamkingdomyoutube islamkingdomnew


Kuma lalle ne idan kun mutu ko kuwa aka kashe ku, haƙĩƙa, zuwa ga Allah ake tãra ku.

Sabõda wata rahama ce daga Allah ka yi sanyin hali a gare su. Kuma dã kã kasance mai hushi mai kaurin zuciya, dã sun wãtse daga għfenka. Sai ka yãfe musu laifinsu, kuma ka nħma musu gãfara, kuma ka yi shãwara da su a cikin al´amarin. Sa´an nan kuma idan ka yi niyyar zartarwa, to, ka dõgara ga Allah, lalle ne, Allah Yana son mãsu tawakkali.

Idan Allah Ya taimake ku, to, bãbu marinjayi a gare ku. Kuma idan Ya yarɓe ku, to, wãnħ ne wanda yake taimakon ku bãyanSa? Kuma ga Allah sai mũminai su dõgara.

Kuma bã ya yiwuwa ga wani annabi ya ci gulũlu. Wanda ya ci gulũlu zai je da abin da ya ci na gulũlun, a Rãnar Ƙiyama. Sa´an nan a cika wa kõwane rai sakamakon abin da ya tsirfanta. Kuma sũ, bã zã a zãlunce su ba.

Shin fa, wanda ya bĩbiyi yardar Allah, yana zama kamar wanda ya kõma da fushi daga Allah kuma makomarsa Jahannama ce? Kuma tir da makõma ita!

Sũ, darajõji ne a wurin Allah, kuma Allah Mai gani ne ga abin da suke aikatawa.

Lalle ne haƙĩƙa Allah Yã yi babbar falala a kan mũminai, dõmin Yã aika a cikinsu, Manzo daga ainihinsu yana karanta ãyõyinSa a gare su, kuma yana tsarkake su, kuma yana karantar da su Littãfi da hikima, kuma lalle, sun kasance daga gabãni, haƙĩƙa suna cikin ɓata bayyananniya.

Shin kuma a lõkacin da wata masĩfa, haƙĩƙa, ta sãme ku alhãli kuwa kun sãmar da biyunta, kun ce: "Daga ina wannan yake?" Ka ce: "Daga wurin rãyukanku yake." Lalle ne, Allah, a kan dukan kõme, Mai ĩkon yi ne.