islamkingdomfaceBook islamkingdomtwitter islamkingdomyoutube islamkingdomnew


Sa´an nan suka jũya da wata ni´ima daga Allah da wata falala, wata cũta ba ta shãfe su ba, kuma suka bi yardar Allah. Kuma Allah ne Ma´abucin falala Mai girma.

Wancan, Shaiɗan ne kawai yake tsõratar da, ku masõyansa. To, kada ku ji tsõronsu, ku ji tsõro Na idãn kun kasance mãsu ĩmãni.

Kuma waɗannan da suke gaugãwa a cikin kãfirci kada su ɓãta maka rai. Lalle ne su, bã zã su cũci Allah da kõme ba. Allah yanã nufin cħwa, bã zai sanya musu wani rabo ba a cikin Lãhira kuma suna da wata azãba mai girma.

Lalle ne, waɗanda suka sayi kãfirci da ĩmani, ba zã su cũci Allah da kõme ba. Kuma sunã da azãba mai raɗaɗi.

Kuma kada waɗanda suka kãfirta su yi zaton cħwa, lalle ne jinkirin da Muke yi musu alhħri ne ga rãyukansu. Munã yi musu jinkirin ne dõmin su ƙãra laifi kawai kuma suna da azãba mai wulãƙantarwa.

Allah bai kasance yana barin mũminai a kan abin da kuke kansa ba, sai Ya rarrabe mummũna daga mai kyau. Kuma Allah bai kasance Yanã sanar da ku gaibi ba. Kuma amma Allah Yana zãɓen wanda Ya so daga manzanninSa. Sabõda haka ku yi ĩmãni da Allah da manzanninSa Kuma idan kun yi ĩmãni kuma kuka yi taƙawa, to, kunã da lãdã mai girma.

Kuma kada waɗannan da suke yin rõwa da abin da Allah Ya bã su daga falalarSa su yi zaton shĩ ne mafi alhħri a gare su. A´a, shĩ mafi sharri ne a gare su. Zã a yi musu saƙandami da abin da suka yi rõwa da Shi a Rãnar Ƙiyãma. Kuma ga Allah gãdon sammai da ƙasa yake, kuma Allah, ga abin da kuke aikatãwa, Masani ne.