islamkingdomfaceBook islamkingdomtwitter islamkingdomyoutube islamkingdomnew


Waɗannan ne waɗanda Allah Ya la´ane su, kuma wanda Allah Ya la´ana to bã zã ka sãmi mataimaki a gare shi ba.

Ko suna da rabõ ne daga mulki? To, a sa´an nan bã zã su iya bai wa mutãne hancin gurtsun dabino ba.

Ko suna hãsadar mutãne ne a kan abin da Allah Ya bã su daga falalarSa? To, lalle ne, Mun bai wa gidan Ibrãhĩm Littãfi da hikima kuma Mun bã su mulki mai girma.

To, daga cikinsu akwai wanda ya yi ĩmãni da shi, kuma daga cikinsu akwai wanda ya kange daga gare shi. Kuma yã isa Jahannama ta hũru da shi.

Lalle ne waɗanda suka kãfirta da ayõyinMu za Mu ƙõne su da wuta, kõ da yaushe fãtunsu suka nuna, sai Mu musanya musu wasu fãtun, dõmin su ɗanɗani azãba. Lalle ne Allah Yã kasance Mabuwãyi, Mai hikima.

Kuma waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyuka na ƙwarai, zã Mu shigar da su gidãjen Aljanna, (waɗanda) ƙõramu sunã gudãna daga ƙarƙashinsu, sunã dawwamammu a cikinsu har abada suna da, a cikinsu, mãtan aure mãsu tsarki, Kuma Munã shigar da su a wata inuwa matabbaciyar lumshi.

Lalle ne Allah Yanã umurnin ku ku bãyar da amãnõni zuwa ga mãsu sũ. Kuma idan kun yi hukunci a tsakãnin mutãne, ku yi hukunci da ãdalci. Lalle ne Allah mãdalla da abin da Yake yi muku wa´azi da shi. Lalle ne Allah Yã kasance Mai ji ne, Mai gani.

Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi ɗã´a ga Allah, kuma ku yi ɗã´a ga ManzonSa, da ma´abũta al´amari daga cikinku. Idan kun yi jãyayya a cikin wani abu, to ku mayar da shi zuwa ga Allah da ManzonSa idan kun kasance kunã ĩmãni da Allah da Rãnar Lãhira. Wannan ne mafi alhħri, kuma mafi kyau ga fassara.