islamkingdomfaceBook islamkingdomtwitter islamkingdomyoutube islamkingdomnew


Shin, ba ka gani ba, zuwa ga waɗanda suke riyãwar cħwa sunã ĩmãni da abin da aka saukar zuwa gare ka da abin da aka saukar daga gabãninka, sunã nufin su kai ƙãra zuwa ga Ɗãgũtu alhãli kuwa, lalle ne, an umurce su da su kãfirta da shi, kuma Shaiɗan yanã nħman ya ɓatar da su, ɓatarwa mai nĩsa.

Kuma idan aka ce musu: "Ku zo zuwa ga abin da Allah Ya saukar, kuma zuwa ga Manzo" zã ka ga munãfukai sunã kange mutãne daga gare ka, kangħwa.

To, yaya, idan wata masĩfa ta sãme su, sabõda abin da hannuwansu suka gabãtar sa´an nan kuma su je maka sunã rantsuwa da Allah cħwa, "Ba mu yi nufin kõme ba sai kyautatawa da daidaitãwa."?

Waɗannan ne waɗanda Allah Ya san abin da ke cikin zukãtansu. Sabõda haka ka kau da kai daga gare su, kuma ka yi musu gargaɗi, kuma ka gaya musu, a cikin sha´anin kansu, magana mai nauyi da fasãha.

Kuma ba Mu aiki wani Manzo ba fãce dõmin a yi masa ɗã´a da izinin Allah. Kuma dã dai lalle sũ a lõkacin da suka zãlunci kansu, sun zo maka sa´an nan suka nħmi gãfarar Allah kuma Manzo ya nħma musu gãfara, haƙĩƙa, dã sun sãmi Allah Mai karɓar tũba Mai jin ƙai.

To, a´aha! Ina rantsuwa da Ubangijinka, ba za su yi ĩmãni ba, sai sun yarda da hukuncinka ga abin da ya sãɓa a tsakãninsu, sa´an nan kuma ba su sãmi wani ƙunci a cikin zukãtansu ba, daga abin da ka hukunta, kuma su sallama sallamãwa.