islamkingdomfaceBook islamkingdomtwitter islamkingdomyoutube islamkingdomnew


Kuma a lõkacin da muka tsĩrar da ku daga mutãnen Fir´auna, su na taya muku muguntar azãba, su na yayyanke ɗiyanku maza su na rãyar da mãtanku. Kuma a cikin wancan akwai jarabawa mai girma daga Ubangijinku.

Kuma a lõkacin da Muka raba tħku sabõda ku, sai Muka tsĩrar da ku kuma Muka nutsar da mutãnen Fir´auna, alhãli kuwa kũ kuna kallo.

Kuma a lõkacin da muka yi wa´adi ga Mũsa, dare arba´in, sa´an nan kuma kuka riƙi maraƙi daga bãyansa, alhãli kũ, kuna mãsu zãlunci (da bauta masa).

Sa´an nan kuma muka yãfe muku daga bãyan wancan, tsammãninku, kuna gõdħwa.

Kuma a lõkacin da Muka baiwa Mũsa Littãfi da rarrabħwa, tsammãninku, kuna shiryuwa.

Kuma a lõkacin da Mũsa ya ce ga mutãnensa: "Ya mutãnena! Lalle ne ku, kun zãlunci kanku game da riƙonku maraƙin, sai ku tũba zuwa ga Mahaliccinku, sai ku kashe kãwunanku. Wancan ne mafi alheri a wajen mahaliccinku. Sa´an nan Ya karɓi tuba a kanku. Lalle ne Shi, Shi ne Mai karɓar tũba, Mai jin ƙai.

Kuma a lõkacin da kuka ce: "Ya Musa! Bã zã mu yi ĩmãni ba dõminka, sai munga Allah bayyane," sabada haka tsãwar nan ta kamaku, alhãli kuwa kuna kallo.

Sa´an nan kuma Muka tãyar da ku daga bãyan mutuwarku, tsammãninku, kuna gõdħwa.

Kuma Muka sanya girgije ya yi inuwa a kanku, kuma Muka saukar da darɓa da tantabaru a kanku; "Ku ci daga mãsu dãɗin abin da Muka azurta ku." kuma ba su zãlunce Mu ba, kuma amma kansu suka kasance suna zãlunta.