islamkingdomfaceBook islamkingdomtwitter islamkingdomyoutube islamkingdomnew


To, sabõda warwarħwarsu ga alkawarinsu, da kãfirtarsu da ãyõyin Allah, da kisansu ga Annabãwa, bã da hakki ba, da maganarsu: "Zukãtanmu sunã cikin rufi." ôa, Allah ne Ya yunƙe a kansu sabõda kãfircinsu, sabõda haka bã zã su yi ĩmãni ba fãce kaɗan.

Kuma sabõda kãfircinsu da faɗarsu, a kan Maryama, ƙiren ƙarya mai girma.

Da faɗarsu : "Lalle ne mu, mun kashe Masĩhu ĩsã ɗan Maryama Manzon Allah," alhãli kuwa ba su kashe shi ba, kuma ba su kħre shi ba, kuma amma an kamanta shi ne a garħ su. Lalle ne waɗanda suka sãɓã wa jũna a cikin sha´aninsa lalle ne, sunã shakka daga gare shi, bã su da wani ilmi fãce bin zato kuma ba su kashe shi ba bisa ga yaƙĩni.

ôa, Allah Ya ɗauke shi zuwa garħ Shi, kuma Allah Yã kasance Mabuwãyi, Mai hikima.

Kuma bãbu kõwa daga Mutãnen Littafi , fãce lalle yanã ĩmãni da shi a gabãnin mutuwarsa, kuma a Rãnar Ƙiyãma yana kasancħwa mai shaida, a kansu.

To, sabõda zãlunci daga waɗanda suka tũba (Yahũdu) Muka haramta musu abũbuwa masu dãɗi waɗanda aka halatta su a gare su, kuma sabõda taushħwarsu daga hanyar Allah da yawa.

Da karɓarsu ga riba, alhãli kuwa an hana su daga gare ta, da cin su ga dũkiyar mutãne daƙarya. Kuma Muka yi tattali, dõmin kãfirai, azãba mai raɗaɗi.

Amma tabbatattu a cikin ilmi daga gare su, da mũminai, suna ĩmani da abin da aka saukar zuwa gare ka, da abin da aka saukar daga gabãninka, madalla da masu tsai da salla, da mãsu bãyar da zakka, da mãsu ĩmãni da Allah da Rãnar Lãhira. Waɗannan zã Mu bã su lãda mai girma.