islamkingdomfaceBook islamkingdomtwitter islamkingdomyoutube islamkingdomnew


Lalle ne waɗanda suka yi ĩmãni, da waɗanda suka tũba*, da Nasãra da Makarkata, wana ya yi ĩmani da Allah da Yinin Lãhira, kuma ya aikata aikin ƙwarai, to, suna da ijãrarsu a wurin Ubangijinsu, kuma bãbu tsõro a kansu, kuma ba su zama suna yin baƙin ciki ba.

Kuma a lõkacin da Muka riƙi alƙawarinku, kuma Muka ɗaukaka dũtse a bisa gareku: "Ku kãma abin da Muka baku da ƙarfi. Kuma ku ambaci abin da yake a cikin sa, tsammãninku ku kãrekanku.

Sa'an nan kuma kuka jũya daga bayan wancan, to, bã dõmin falalar Allah ba da rahamarSa a kanku, haƙĩƙa, dã kun kasance daga mãsu hasãra."

Kuma lalle ne, haƙĩƙa, kun san waɗanda suka ƙẽtare haddi daga gare ku a cikin Asabar, sai muka ce musu: "ku kasance birai ƙasƙantattu."

Muka sanya ta (mas'alar) azãba, dõmin abin da yake gaba gareta, da yake a bãyanta, kuma wa'azi ga mãsu taƙawa.

Kuma a lõkacin da Musa yace ga mutanensa: "Lalle ne, Allah Yana umurtar ku da ku yanka wata sãniya." Suka ce: "Shin kana riƙon mu ne da izgili?" Ya ce: "Ina nẽman tsari daga Allah da in kasance daga jãhilai."

Suka ce: "Ka rõƙa mana Ubangijinka, Ya bayyana mana, mecẽ ce ita?" Ya ce: "Lalle ne, Shi, Yana cewa: "Lalle ne ita sãniya ce; bã tsõfuwa ba, bã kuma budurwa ba, tsakãtsaki ce a tsakãnin wancan,' sai ku aikata abin da ake umurninku."

Suka ce: "Ka rõƙa mana Ubangijinka Ya bayyana mana abin da yake launinta." Ya ce: "Lalle ne, Shi Yana cewa: "Ita wata saniya ce fatsa-fatsa, mai tsan-tsan launi, tana faranta ran mausu kallonta."