islamkingdomfaceBook islamkingdomtwitter islamkingdomyoutube islamkingdomnew


Lalle ne, Allah ne Mai ts?gewar ƙw?yar hatsi da kwalfar gurtsu. Yan? fitar da mai rai daga mamaci, kuma (Shi) Mai fitar da mamaci ne daga mai rai. Wannan ne Allah. To, yãya ake karkatar da ku?

Mai tsãgħwar sãfiya, kuma Ya sanya dare mai natsuwa, kuma da rãna da watã a bisa liss?fi. Wannan ne ƙaddarãwar Mabuwãyi Masani.

Kuma Shi ne Ya sanya muku taurãri dõmin ku shiryu da su a cikin duffan tudu da ruwa. Lalle ne Mun bayyana ãyõyi daki-daki, ga mutãne waɗanda suke sani.

Kuma Shi ne Ya ƙãga halittarku daga rai guda, sa´an nan da mai tabbata da wanda ake ajħwa. Lalle ne Mun bayyanã ãyõyi daki-daki, ga mutãne waɗanda suke fahimta.

Kuma Shi ne Ya saukar da ruwa daga sama, Muka fitar da tsiron dukkan kõme game dã shi, sa´an nan Muka fitar da kõre daga gare shi, Muna fitar da kwãya ɗamfararriya daga gare shi (kõren), kuma daga dabĩno daga hirtsinta akwai dumbuje-dumbuje makusanta, kuma (Muka fitar) da gõnaki na inabõbi da zãitũni da rummãni, mãsu kamã da jũna da wasun mãsu kama da jũna. Ku dũba zuwa ´ya´yan itãcensa, idan ya yi ´ya´yan, da nunarsa. Lalle ne a cikin wannan akwai ãyõyi ga waɗanda suke yin ĩmãni.

Kuma suka sanya wa Allah abõkan tãrayya, aljannu, alhãli kuwa (Shi) Ya halitta su. Kuma sun ƙirƙira masa ɗiya da ´yã´ya, bã da ilmi ba. TsarkinSa yã tabbata! Kuma Ya ɗaukaka daga abin da suke sifantãwa.

Mafarin halittar sammai da ƙasa. Yãya ɗã zai zama a gare Shi alhãli kuwa mãta ba ta kasance ba, a gare Shi, kuma Ya halitta Dukkan k?me, kuma Shĩ, game da dukan kõme, Masani ne?