islamkingdomfaceBook islamkingdomtwitter islamkingdomyoutube islamkingdomnew


Dõmin haka wanda Allah Ya yi nufin ya shiryar da shi sai ya bũɗa ƙirjinsa dõmĩn Musulunci, kuma wanda Ya yi nufin Ya ɓatar da shi, sai Ya sanya ƙirjinsa mai ƙunci matsattse, kamar dai yanã tãkãwa ne a ckin sama. Kamar wannan ne Allah Yake sanyãwar ƙazanta a kan waɗanda bã su yin ĩmãni.

Wannan ita ce hanya ta Ubangijinka madaidaiciya. Lalle ne Mun bayyana ãyõyi daki-daki ga mutãne mãsu karɓar tunãtarwa.

Sunã da gidan aminci a wurin Ubangjinsu, kuma Shĩ ne Majiɓincinsu, sabõda abin da suka kasance sunã aikatãwa.

Kuma rãnar da yake tãra su gaba ɗaya (Yanã cħwa): "Yã jama´ar aljannu! Lalle ne kun yawaita kanku daga mutãne." Kuma majiɓantansu daga mutãne suka ce: "Yã Ubangjinmu! Sãshenmu ya ji dãɗi da sãshe, kuma mun kai ga ajalinmu wanda Ka yanka mana!" (Allah) Ya ce: "Wuta ce mazaunarku, kunã madawwama a cikinta, sai abin da Allah Ya so. Lalle ne Ubangijinka Mai hikima ne, Masani."

Kuma kamar wancan ne Muke jiɓintar da sãshen azzãlumai ga sãshe, sabõda abin da suka kasance sunã tãrãwa.

Yã jama´ar aljannu da mutãne! Shin, manzanni daga gare ku ba su jħ muku ba sunã lãbarta ãyõyiNa a kanku, kuma sunã yi muku gargaɗin haɗuwa da wannan yini nãku? Suka ce: "Mun yi shaida a kan kãwunanmu." Kuma rãyuwar dũniya tã rũɗħ su. Kuma suka yi shaida a kan kãwunansu cħwa lalle ne sũ, sun kasance kãfirai.