islamkingdomfaceBook islamkingdomtwitter islamkingdomyoutube islamkingdomnew


Wancan kuwa sabõda Ubangijinka bai kasance Mai halaka alƙaryõyi sabõda wani zãlunci ba ne, alhãli kuwa mutãnensu sunã jãhilai.

Kuma ga kõwanne, akwai darajõji daga abin da suka aikata. Kuma Ubangijinka bai zama mai shagala ba daga abin da suke aikatãwa.

Kuma Ubangijinika Wadãtacce ne Ma´abũcin rahama. Idan Yã so zai tafi da ku, kuma Ya musanya daga bãyanku, abin da Yake so, kamar yadda Ya ƙãga halittarku daga zũriyar wasu mutãne na dabam.

Lalle ne abin da ake yi muku wa´adi lalle mai zuwa ne kuma ba ku zama mãsu buwãya ba,

Ka ce: "Yã ku mutãnena! Ku yi aiki a kan halinku, lalle ne nĩ mai aiki ne, sa´an nan da sannu zã ku san wanda ãƙibar gida zã ta kasance a gare shi. Lalle ne shi, azzãlumai bã zã su ci nasarã ba."

Kuma sun sanya wani rabõ ga Allah daga abin da Ya halitta daga shũka da dabbõbi, sai suka ce: "Wannan na Allah ne," da riyãwarsu "Kuma wannan na abũbuwan shirkinmu ne." Sa´an nan Abin da ya kasance na abũbuwan shirkinsu, to, bã ya sãduwa zuwa Allah, kuma abin da ya kasance na Allah, to, shĩ yanã sãduwa zuwa ga abũbuwan shirkinsu. Tir da hukuncinsu!

Kuma kamar wancan ne abũbuwan shirkinsu suka ƙãwata wa mãsu yawa, daga mãsu shirkin; kashewar ´ya´yansu, dõmin su halaka su kuma dõmin su rikitar da addininsu a gare su, kuma dã Allah Yã so dã ba su aikatã shi ba. Sabõda haka ka bar su da abin da suke ƙirƙirãwa.