islamkingdomfaceBook islamkingdomtwitter islamkingdomyoutube islamkingdomnew


A. L̃. M̃. Ṣ̃.

Littãfi ne aka saukar zuwa gare ka, kada wani ƙunci ya kasance a cikin ƙirjinka daga gare shi, dõmin ka yi gargaɗi da shi. Kuma tunãtarwa ne ga mũminai.

Ku bi abin da aka saukar zuwa gare ku daga Ubangijinku, kuma kada ku dinga bin wasu majiɓinta baicinSa. Kaɗan ƙwarai kuke tunãwa.

Kuma da yawa wata alƙarya Muka halaka ta, sai azãbarMu ta jħ mata da dare kõ kuwa sunã mãsu ƙailũla.

Sa´an nan bãbu abin da yake da´awarsu, a lõkacin da azãbarMu ta jħ musu, fãce suka ce: "Lalle ne mũ muka kasance mãsu zãlunci,"

Sa´an nan lalle ne Munã tambayar waɗanda aka aika zuwa gare su, kuma lalle Munã tambayar Manzannin.

Sa´an nan haƙĩƙa Munã bã su lãbãri da ilmi kuma ba Mu kasance mãsu fakuwa ba.

Kuma awo a rãnar nan ne gaskiya. To, wanda sikħlansa suka yi nauyi, to, waɗannan sũ ne mãsu cin nasara.

Kuma wanda sikħlansa suka yi sauƙi, to, waɗannan ne waɗanda suka yi hasarar rayukansu, sabõda abin da suka kasance, da ãyõyinMu, sunã yi na zãlunci.

Kuma lalle ne haƙĩƙa, Mun sarautar da ku, a cikin ƙasa, kuma Mun sanya muku abũbuwan rãyuwa, a cikinta; kaɗan ƙwarai kuke gõdħwa.

Kuma lalle ne haƙĩƙa Mun halittã ku sa´an nan kuma Mun sũrantã ku, sa´an nan kuma Mun ce wa malã´iku: "Ku yi sujada ga Ãdam." Sai suka yi sujada fãce Iblĩs, bai kasance daga mãsuyin sujadar ba.