islamkingdomfaceBook islamkingdomtwitter islamkingdomyoutube islamkingdomnew


Kuma a lõkacin da wani Littãfi daga wurin Allah ya je musu, mai gaskatãwa ga abin da yake tãre da su, alhãli kuwa sun kasance daga gabãnin haka suna fãtar taimako da shi a kan waɗanda suka kãfirta. To, a lõkacin da abin da suka sani ya je musu, sai suka kãfirta da shi. Sabõda haka la´anar Allah ta tabbata a kan kãfirai.

Tir da abin da suka sayi rãyukansu da shi; watau su kãfirta da abin da Allah Ya saukar sabõda zãlunci; kada Allah Ya saukar da falalarsa a kan wanda Yake so daga bãyinsa. Sai suka kõmo da fushi game da wani fushi. Kuma ga kãfirai akwai azãba mai wulãƙantarwa.

Kuma idan aka ce musu: "Ku yi ĩmãni da abin da Allah Ya saukar." Sai su ce: "Muna ĩmãni da abin da aka saukar a gare mu," kuma suna kãfircħwa da abin da ke bãyansa, alhãli kuwa, shi ne gaskiyar (da suka sani) mai gaskatawa ga abin da yake tãre da su (na Attaura). Ka ce: "To, don me kuke kashe annabãwan Allah gabãnin wannan, idan kun kasance mãsu bãyar da gaskiya?"

Kuma lalle ne haƙĩƙa Mũsã ya zo muku da hujjõji bayyanannu, sa´an nan kuka riƙi maraƙi daga bãyansa, alhãli kuwa kuna mãsu zãlunci.

Kuma a lõkacin da Muka riƙi alkawarinku kuma Muka ɗaukaka dutse a bisa gare ku, (Muka ce:) "Ku riƙi abin da Muka kãwo muku da ƙarfi kuma ku ji" Suka ce: "Mun ji kuma mun ƙi." Kuma aka zuba son maraƙin a cikin zukatansu sabõda kãfircinsu. Ka ce: "Tir da abin da ĩmãninku yake umurnin ku da shi, har idan kun kasance mãsu ĩmãni!"