islamkingdomfaceBook islamkingdomtwitter islamkingdomyoutube islamkingdomnew


Suka ce: "Ya Ubangijinmu! Mun zãlunci kanmu. Kuma idan ba Ka gãfarta mana ba, kuma Ka yi mana rahama, haƙĩƙa, Munã kasancħwa daga mãsu hasãra."

Ya ce: "Ku sauka, s?shenku zuwa ga s?she yan? maƙiyi, kuma kun? da matabbata a cikin ƙasa, da ɗan jin d?ɗi zuwa ga wani l?kaci."

Ya ce: "A cikinta kuke rãyuwa, kuma a cikinta kuke mutuwa, kuma daga gare ta ake fitar da ku."

Yã ɗiyan Ãdam! Lalle ne Mun saukar da wata tufa a kanku, tanã rufe muku al´aurarku, kuma da ƙawã. Kuma tufar taƙawa wancan ce mafi alhħri. Wancan daga ãyõyin Allah ne, tsammãninsu sunã tunãwa!

Yã ɗiyan Ãdam! Kada Shaiɗan, lalle, ya fitine ku, kamar yadda ya fitar da iyãyenku, biyu daga Aljanna, yanã fizge tufarsu daga gare su, dõmin ya nũna musu al´aurarsu. Lalle ne shĩ, yanã ganin ku, shi da rundunarsa, daga inda bã ku ganin su. Lalle ne Mũ, Mun sanya Shaiɗan majiɓinci ga waɗanda bã su yin ĩmãni.

Kuma idan suka aikata alfãsha su ce: "Mun sãmi ubanninmu a kanta." Kuma Allah ne Ya umurce mu da ita."Ka ce: "Lalle ne, Allah bã Ya umurni da alfãsha. Shin kunã faɗar abin da bã ku da saninsa ga Allah?"

Ka ce: "Ubangjina Yã yi umurni da ãdalci; kuma ku tsayar da fuskõkinku a wurin kõwane masallãci, kuma ku rõƙħ Shi, kunã mãsu tsarkake addini gare Shi. Kamar yadda Ya fãra halittarku kuke kõmãwa."

Wata ƙungiya (Allah) Yã shiryar, kuma wata ƙungiya ɓata tã wajaba a kansu; lalle ne sũ, sun riƙi shaiɗanu majiɓinta, baicin Allah, kuma sunã zaton, lalle sũ, mãsu shiryuwa ne.