islamkingdomfaceBook islamkingdomtwitter islamkingdomyoutube


A. L̃. R. Waɗancan ãyõyin littãfi ne kyautatacce.

Shin, yã zama abin mãmaki ga mutãne dõmin Mun yi wahayi zuwa ga wani namiji daga gare su cħwa, "Ka yi gargaɗi ga mutãne kuma ka yi bushãra ga waɗanda suka yi ĩmãni da cħwa: Lalle ne sunã da abin gabãtarwar gaskiya a wurin Ubangijinsu."Kãfirai suka ce: "Lalle ne wannan, haƙĩƙa, masihirci ne bayyananne."

Lalle Allah ne Ubangijinku wanda Ya halicci sammai da ƙasa a cikin kwãna shida, sa´an nan kuma Ya daidaita a kan Al´arshi Yanã gudãnar da al´amari. Bãbu wani macħci fãce a bayan izninSa. Wannan ne Allah, Ubangijinku, sai ku bauta Masa. Shin fa, ba ku tunãni?

Zuwa gare Shi makõmarku take gabã ɗaya, wa´adin Allah gaskiya ne. Haƙĩƙa, Shi ne Yake fara halitta, sa´an nan kuma Ya mayar da ita dõmin Ya sãka wa waɗanda suka yi ĩmãni kuma suka aikata ayyukan ƙwarai da ãdalci, kuma waɗanda suka kãfirta sunã da abin sha daga ruwan zãfi, da azãba mai raɗaɗi, sabõda abin da suka kasance sunã yi na kãfirci.

Shĩ ne wanda Ya sanya muku rãnã, babban haske, da watã mai haske, kuma Ya ƙaddara shi ga Manzilõli, dõmin ku san ƙidãyar shħkaru da lissãfi. Allah bai halitta wannan ba, fãce da gaskiya, Yanã bayyana ãyõyi daki-daki dõmin mutãne waɗanda suke sani.

Lalle ne a cikin sãɓãwar dare da yini, da abin da Allah Ya halitta a cikin sammai da ƙasa, haƙĩƙa akwai ãyõyi ga mutãne waɗanda suke yin taƙawa.