islamkingdomfaceBook islamkingdomtwitter islamkingdomyoutube


Kuma idan Allah Ya shãfe ka da wata cũta, to, bãbu mai yãyħ ta fãce shi, kuma idan Yanã nufin ka da wani alhħri, to, bãbu mai mayar da falalarSa. Yanã sãmun wanda Yake so daga cikin bãyinSa da shi. Kuma Shĩ ne Mai gãfara, Mai jin ƙai.

Ka ce: "Yã ku mutãne! Lalle ne gaskiya, ta zo muku daga Ubangijinku. To, wanda ya shiryu, yã shiryu ne dõmin kansa kawai, kuma wanda ya ɓace yana ɓacewa ne a kansa kawai. Kuma ban zama wakĩli a kanku ba."

Kuma ka bi abin da ake yin wahayinsa zuwa gare ka, kuma ka yi haƙuri har Allah Ya yi hukunci. Kuma Shĩ ne Mafi alhħrin mãsu hukunci.

A. L̃. R. Littãfi ne an kyautata ãyõyinsa, sa´an nan an bayyanã su daki-daki, daga wurin Mai hikima, Mai ƙididdigewa.

Kada ku bautã wa kõwa fãce Allah. Lalle ne ni a gare ku mai gargaɗi ne kuma mai bushãrã daga gare Shi.

Kuma ku nħmi gãfara gun Ubangijinku. Sa´an nan ku tũba zuwa gare Shi, Ya jiyar da ku dãɗi, jiyarwa mai kyau zuwa ga ajali ambatacce, kuma Ya bai wa dukkan ma´abucin, girma girmansa. Amma idan kun jũya, to, lalle nĩ, inã tsõron azãbar yini mai girma a kanku.

Zuwa ga Allah makõmarku take, kuma Shĩ a kan kõme Mai ĩkon yi ne.

To, lalle sũ sunã karkatar da ƙirjinsu dõmin su ɓõye daga gare shi. To, a lõkacin da suke lulluɓħwa da tufãfinsu Yanã sanin abin da suke ɓoyewa da abin da suke bayyanãwa. Lalle Shi Masani ne ga abin da yake a cikin ƙirãzã.