islamkingdomfaceBook islamkingdomtwitter islamkingdomyoutube


Suna tambayar ka ga ganĩma. ka ce: "Ganĩma ta Allah da ManzonSa ce. Sai ku bi Allah da taƙawa, kuma ku gyãra abin da yake a tsakãninku, kuma ku yi ɗã´a ga Allah da ManzonSa, idan kun kasance mũminai."

Abin sani kawai, mũminai sũ ne waɗanda suke idan an ambaci Allah, zukãtansu su firgita, kuma idan an karanta ãyõyinSa a kansu, su ƙãrã musu wani ĩmãni, kuma ga Ubangijinsu suke dõgara.

Waɗanda suke tsayar da salla, kuma daga abin da Muka azũrtã su sunã ciyarwa.

Waɗannan sũ ne mũminai da gaskiya. Sunã da darajõji a wurin Ubangijinsu, da wata gãfara da arziki na karimci.

Kamar yadda Ubangijinka Ya fitar da kai daga gidanka da gaskiya, alhãli kuwa lalle wani ɓangare na mũminai, haƙĩƙa, sunã ƙyãma.

Sunã jãyayya da kai a cikin (sha´anin) gaskiya a bãyan tã bayyanã, kamar dai lalle anã kõra su zuwa ga mutuwa ne alhãli kuwa sunã kallo.

Kuma a lõkacin da Allah Yake yi muku alkawari da ɗayan ƙungiya biyu, cħwa lalle ita tãku ce: kuma kunã gũrin cħwa lalle ƙungiya wadda bã ta da ƙaya ta kasance gare ku, kuma Allah Yanã nufin Ya tabbatar da gaskiya da kalmõminSa, kuma Ya kãtse ƙarshen kãfirai;

Dõmin Ya tabbatar da gaskiya, kuma Ya ɓãta ƙarya, kuma kõdã mãsu laifi sun ƙi.