islamkingdomfaceBook islamkingdomtwitter islamkingdomyoutube


Barranta daga Allah da ManzonSa zuwa ga waɗanda kuka yi wa alkawari daga mãsu shirki

Sabõda haka ku yi tafiya a cikin ƙasa watã huɗu, kuma ku sani lalle kũ, bã mãsu buwãyar Allah ba ne, kuma lalle Allah ne Mai kunyatar da kãfirai.

Kuma da yħkuwa daga Allah da ManzonSa zuwa ga mutãne, a Rãnar Haji Babba cħwa lallene Allah Barrantacce ne daga mãsu shirki, kuma ManzonSa (haka). To, idan kun tũba to shi ne mafi alhħri a gare ku, kuma idan kun jũya, to, ku sani lalle ne kũ, bã mãsu buwãyar Allah ba ne. Kuma ka bãyar da bishãra ga waɗanda suka kãfirta, da azãba mai raɗaɗi.

Sai waɗanda kuka yi wani alkawari daga mãsu shirki, sa´an nan kuma ba su rage ku da kõme ba, kuma ba su taimaki kõwa a kanku ba, to, ku cika alkawarin, zuwa gare su, har ga iyakar yarjħjħyarsu. Lalle ne Allah Yanã son mãsu taƙawa.

Kuma idan watanni, mãsu alfarma suka shige, to, ku yãki mushirikai inda kuka sãmħ su, kuma ku kãmã su, kuma ku tsare su, kuma ku zaune musu dukkan madãkata. To, idan sun tũba, kuma suka tsayar da salla, kuma suka bãyar da zakka to ku sakar musu da hanyarsu. Lalle Allah ne Mai gãfara,Mai jin ƙai.

Idan wani daga mushirikai ya nemi maƙwabtakarka to, ka ba shi maƙwabtakar har ya ji, maganar Allah, sa´an nan ka isar da shi ga wurin amincewarsa. Wancan fa domin lalle ne su, mutãne ne waɗanda ba su sani ba.