Surah [ An-nisa'i ] ayah [106] Kuma ka nħmi Allah gãfara. Lalle ne Allah Yã kasance Mai gãfara, Mai jin ƙai.
Surah [ Aal-imraan ] ayah [103] Kuma ku yi daidami da igiyar Allah gabã ɗaya, kuma kada ku rarraba. Kuma ku tuna ni´imar Allah a kanku a lõkacin da kuka kasance maƙiya sai Ya sanya sõyayya a tsakãnin zukãtanku sabõda haka kuka wãyi gari, da ni´imarSa, ´yan´uwa. Kuma kun kasance a kan gãɓar rãmi na wutã sai Ya tsãmar da ku daga gare ta. Kamar wannan ne Allah Yake bayyana muku ayõyinSa, tsammãninku, zã ku shiryu.
Surah [ Al-baqara ] ayah [179] Kuma kuna da rãyuwa a cikin ƙisãsi, yã ma´abuta hankula; tsammãninku, zã ku yi taƙawa.
Surah [ Luqman ] ayah [19] "Kuma ka tsakaita a tafiyarka, kuma ka runtse ga sautinka. Lalle mafi mũnin sautuka haƙĩƙa shĩ ne sautin jãkuna. "
Surah [ Al-anfaal ] ayah [33] Kuma Allah bai kasance Yanã yi musu azãba ba alhãli kuwa kai kanã cikinsu, kuma Allah bai kasance Mai yi musu azãba ba alhãli kuwa sunã yin istigfãri.