Surah [ Al-hadeed ] ayah [21] Ku yi tsħre zuwa ga (nħman) gãfara daga Ubangjinku, da Aljanna fãɗinta kamar fãɗin samã da ƙasã ne, an yi tattalinta dõmin waɗanda suka yi ĩmãni da Allah da ManzanninSa. Wannan falalar Allah ce, Yanã bãyar da ita ga wanda Ya so. Kuma Allah Mai falala ne Mai girma.
Surah [ Az-zukhruf ] ayah [80] Ko sunã zaton lalle Mũ, bã Mu jin asĩrinsu da gãnãwarsu? Na´am! Kuma manzannin Mu na tãre da su sunã rubũtãwa.
Surah [ Az-zumar ] ayah [22] Shin fa, wanda Allah Ya buɗa ƙirjinsa, dõmin Musulunci sa´an nan shi yanã a kan haske daga Ubangijinsa, (zai zama kamar waninsa)? To, bone yã tabbata ga maƙeƙasa zukãtansu daga ambaton Allah. Waɗancan sunã a cikin wata ɓata bayyananna.
Surah [ Fussilat ] ayah [53] Zã Mu nũna musu ãyõyinMu a cikin sãsanni da kuma cikin rãyukansu, har ya bayyana a gare su cħwã lalle (Alƙur´ãni), shi ne gaskiya. Ashe, kuma Ubangijinka bai isa ba, ga cħwa lalle Shĩ halartacce ne a kan kowane abu ne?
Surah [ Al-kahf ] ayah [10] A lõkacin da samarin suka tattara zuwa ga kõgon, sai suka ce: "Ya Ubangijinmu! Ka bã mu wata rahama daga gare Ka, kuma Ka sauƙaƙe mana (sãmun) shiriya daga al´amarinmu."