Surah [ Fussilat ] ayah [34] Kuma kyautatãwa bã ta daidaita kuma haka mũnanãwa. Ka tunkuɗe cũta da abin da yake mafi kyau, sai ga shi wanda akwai ƙiyayya a tsakaninka da tsakaninsa, kamar dai shi majibinci ne, masoyi.
Surah [ Houd ] ayah [47] Ya ce: "Yã Ubangijina! Lalle ne nĩ, inã nħman tsari gare Ka da in tambaye Ka abin da bã ni da wani ilmi a kansa. Idan ba Ka gãfarta mini ba, kuma Ka yi mini rahama, zan kasance daga mãsu hasãra."
Surah [ Yusuf ] ayah [101] "Yã Ubangijina lalle ne Kã bã ni daga mulki, kuma Kã sanar da ni daga fassarar lãbaru. Ya Mahaliccin sammai da ƙasa! Kai ne Majiɓincĩna a dũniya da Lãhira Ka karɓi raina inã Musulmi, kuma Ka riskar da ni ga sãlihai."
Surah [ An-nisa'i ] ayah [19] Ku waɗanda suka yi ĩmãni! Bã ya halatta a gare ku, ku gãji mãtã a kan tĩlas kuma kadaku hana su aure dõmin ku tafi da sãshen abin da kuka ba su, fãce idan suka zo da wata alfãsha bayya nanniya kuma ku yi zamantakħwa da su da alhħri sa´an nan idan kun ƙĩ su, to akwai tsammãnin ku ƙi wani abu alhãli kuwa Allah Ya sanya wani alhħri mai yawaa cikinsa.
Surah [ At-taubah ] ayah [129] To, idan sun jũya, sai ka ce: Ma´ishĩna Allah ne. Bãbu abin bautãwa fãce shi. A gare Shi nake dõgara. Kuma Shi ne Ubangijin Al´arshi mai girma.