Imani da sunayen Allah kyawawa, tare da sharhin wasu daga cikinsu.


7692
Surantawa
Yana daga cikin bayar da gaskiya da Allah, bayar da gaskiya da sunayensa mafiya kyau, da siffofinsa mafiya xaukaka, ba tare da jirkirta su ba, ko kamanta su da na bayi, ko kore su ba, kuma wadannan sunaye nasa sun tattara dukkan siffofi na cika da tumbatsa wadanda ya wajaba ga bayi su sun maanoninsu domin sanin ubangiji da hakkokinsa.

Manufofin huxubar

Kwaxaitarwa a kan imani da sunayen Allah Ta’ala.

Sharhin ma’anonin wasu daga cikin sunayen Allah Ta’ala.

Kwaxaitarwa a kan yin addu’a da sunayen Allah Ta’ala.

Bayani a kan cewa sunayen Allah shi ne ya kira kansa da su. Hankali baya gano su.

Huxuba Ta Farko

Dukkan yabo da godiya da kirari sun tabbata ga Allah, taimakonsa da gafararsa muke nema, kuma muna neman tsarinsa daga sharrin kawukanmu da munanan ayyukanmu. Wanda Allah ya shiryar babu mai vatar da shi, wanda kuma ya vatar to babu mai shiryar da shi. Kuma ina shaidawa babu abin bauta da gaskiya sai Allah, shi kaxai ne ba shi da abokin tarayya. Kuma ina shaidawa cewa, Annabi Muhammadu bawansa ne manzonsa ne. (Yaku waxanda suka yi imani ku ji tsoron Allah yadda ya cancaci a ji tsoronsa, kada ku mutu face kuna musulmi). (Ya ku mutane ku ji tsoron Ubangijinku wanda ya halicceku daga rai guda xaya, kuma ya ya halicci matarsa daga gare shi, kuma ya yaxa maza da mata daga garesu (su biyu). Ku ji tsoron Allah wanda kuke yiwa junanku magiya da shi, (kuma ku kiyaye) zumunci. Lalle Allah mai kula ne da ku). (Yaku wanxanda suka yi imani ku ku ji tsoron Allah kuma ku faxi magana ta daidai. Sai Allah ya gyara muku ayyukanku, kuma ya gafarta muku zunubbanku. Wanda ya bi Allah da Manzonsa haqiqa ya rabauta rabauta mai girma). Bayan haka, lalle mafi gaskiyar magana maganar Allah, kuma mafi kyawon shiriya shiriyar Annab Muhammadu (ﷺ). Kuma mafi shirrin al'amura (a addini) qagaggunsu, kuma duk wani qagaggen abu (a addini) bidi'a ce, duk wata bidi'a vata ce, duka wani vata kuma yana wuta".

Bayan haka:

Ya ku bayin Allah! Yana daga cikin bayar da gaskiya da Allah, bayar da gaskiya da sunayensa mafiya kyau, da siffofinsa mafiya xaukaka, ba tare da jirkirta su ba, ko kamanta su da na bayi, ko kore su ba. Ubangiji ya ce,

(وَلِلَّهِ الْأَسْمَاءُ الْحُسْنَى فَادْعُوهُ بِهَا180) [الأعراف: ١٨٠].

(Sunaye mafiya kyau sun tabbata ga Allah, don haka ku roqe shi da su).

Kuma Ubangiji ya ce,

(وَلَا تَقْفُ مَا لَيْسَ لَكَ بِهِ عِلْمٌ36) [الإسراء: ٣٦].

(Kada ka bibiyi abin da ba ka da sani a kansa).

Kuma Manzon Allah (ﷺ) ya faxa a cikin fitaccen hadisinsa, cewa “Ya Ubangiji! Ina roqon ka da duk wani sunan da yake naka ne, ka ambaci kanka da shi, ko ka saukar da shi a cikin littafinka, ko ka sanar da shi ga wani daga cikin halittarka, ko ka kevanta da sanin sa cikin sanin gaibu da yake wajenka.” Ahmad da Ibni Hibban suka rawaito shi, kuma hadisi ne ingantacce.

Yana daga cikin sunayen Allah, Allahu: Ma’anarsa: Wanda zukata suke bauta masa, tare da soyayya da qauna da girmamawa. Daga ciki akwai Ar-rahman Ar-rahim: Ma’anarsu: Wanda yake jin qan bayinsa, sama da yadda mahaifiya take jin qan xanta. Ba wata rahama da za ta samu, sai daga rahamarsa, ba wata musiba da za a ije ta, sai da rahamarsa. Ubangiji ya ce,

(وَمَا بِكُمْ مِنْ نِعْمَةٍ فَمِنَ اللَّهِ53) [النحل: ٥٣].

(Duk wani abu da yake tattare da ku na ni’ima, daga Allah yake).

Daga cikinsu, akwai Almaliku: Wanda ya mallaki duniya gabaxayanta, samanta da qasanta. Ba wani abu da zai yi motsi, sai da saninsa da yardarsa. Ubangiji ya ce,

(قُلِ اللَّهُمَّ مَالِكَ الْمُلْكِ تُؤْتِي الْمُلْكَ مَنْ تَشَاءُ26) [آل عمران: ٢٦].

(Ka ce, “Ya Allah, mamallakin mulki! Kana bayar da mulki ga wanda ka so). Kuma Ubangiji ya ce,

(مَالِكِ يَوْمِ الدِّينِ4) [الفاتحة: 4]

(Mamallakin ranar sakamako).

Kuma yana daga cikin sunayensa, Alquddusu: Shi ne wanda ya tsarkaka daga dukkan tawaya da aibuka. Ya halicci halitta gabaxayanta, wahala ba ta shafe shi ba, ko cuta. Ubangiji ya ce,

(وَلَقَدْ خَلَقْنَا السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضَ وَمَا بَيْنَهُمَا فِي سِتَّةِ أَيَّامٍ وَمَا مَسَّنَا مِنْ لُغُوبٍ38) [ق: 38] (Haqiqa mun halicci sammai da qasa da abin da yake tsakanin su, cikin kwanaki shida, kumsa wahala ba ta shafe mu).

Daga cikin sunayensa, akwai Alqawiyyu, Alqahhaar: Babu wani abin halitta, face sai yana qarqashin ikonsa da tanqwarawarsa, babu wani mai ji-ji-da-kai, face sai ya risuna ga girmansa da qarfinsa. Ubangiji ya ce,

(مَا قَدَرُوا اللَّهَ حَقَّ قَدْرِهِ إِنَّ اللَّهَ لَقَوِيٌّ عَزِيز74)ٌ [الحج: 74]

(Ba su girmama Allah yadda ya cancanta su girmama shi ba. Lallai Allah mai qarfi ne, kuma mabuwayi).

Yana daga cikin sunayensa, Al-Aliim: Wanda ya san abin da yake voye, kuma ya san abin da yake sarari, da abin da yake cikin teku. Babu wani ganye da zai faxi, face sai ya sani, babu wata qwaya da take cikin duhun qasa, ko xanyen abu ko busasshe, face yana cikin littafi mabayyani.

Yana daga cikin sunayensa, Al-Aliyyu A’alaa: Maxaukaki a cikin zatinsa, sama da al-arshinsa, maxaukaki a cikin siffofinsa. Tsarki ya tabbata a gare shi!

Daga cikin sunayensa, akwai Aljabbaar: Wanda yake xora karyayye da mai rauni, kuma yake damqar mai qarfi, ya tanqwara shi.

Daga cikin sunayensa akwai Alghafuur: Wanda yake gafarta zunubai gabaxaya, kuma yake lulluve aibuka, ko da kuwa suna da yawa. Ya zo a cikin hadisi qudusi, Ubangiji ya ce, “Ya xan Adam! Matuqar ka roqe ni, ka qaunaci gafarata, zan gafarta maka, bisa ga abin da ya kasance na laifinka, kuma ban damu ba.” [Tirmizi da Ahmad ne suka ruwaito shi].

Kuma yana daga cikin sunayensa, Alhakiimu: Mai azanci cikin shari’arsa da qaddararsa.

Yana daga cikin sunayensa, Alghaniyyu: Mawadacin da zatinsa daga halittunsa baki xaya.

‘Yan uwa masu sauraro! Ku sani, yana daga cikin imani da sunayen Allah, roqon sa da su, kamar yadda Allah ya ce,

(وَلِلَّهِ الْأَسْمَاءُ الْحُسْنَى فَادْعُوهُ180) [الأعراف: ١٨٠].

(Sunaye mafiya kyau sun tabbata ga Allah, ku roqe shi da su).

Wata rana, Manzon Allah (ﷺ) ya ji wani mutum yana addu’a, yana cewa, “Ya Allah! Lallai ni ina roqon ka da cewa godiya ta tabbata gare ka, babu abin bauta bisa ga cancanta sai kai kaxai, babu abokin tarayya gare ka, mai kyauta, maqagin sama da qasa. Ya ma’abocin girma da karamci! Ya rayayyen sarki, kuma tsayayye!!” Sai Manzon Allah (ﷺ) ya ce, “Haqiqa ya roqi Ubangiji da sunansa mai girma, wanda idan aka roqe shi da shi, yake amsawa, kuma idan aka roqe shi da shi, yake bayarwa.” [Abu Dawud ya rawaito shi].

Ya kai bawan Allah! Ya zama wajibi a kanka, ka riqa roqon Allah, da sunayensa da siffofinsa.

Game da faxar Allah da y ace,“….ku roqe shi da su.” Sheikh Usaimin yana cewa, “Ka sanya su tsani zuwa ga abin da kake nema. Ka zavi sunan da ya dace da buqatarka: Idan za ka roqi gafara, sai ka ce, “Ya mai gafara! Gafarta mini.” Bai dace ba ka ce, “Ya mai tsananin uquba! Ka gafarta mini.” Yin haka, ya yi kama da ba’a. Sai dai ka ce, “Ka kuvutar da ni daga azabarka”…"

Ubangiji yana cewa,

(وَلِلَّهِ الْأَسْمَاءُ الْحُسْنَى فَادْعُوهُ بِهَا وَذَرُوا الَّذِينَ يُلْحِدُونَ فِي أَسْمَائِهِ سَيُجْزَوْنَ مَا كَانُوا يَعْمَلُونَ180) [الأعراف: 180]

(Sunaye mafiya kyau sun tabbata ga Allah, ku roqe shi da su, ku qyale waxanda suke kangara a cikin sunayensa, da sannu za a saka musu da abin da suke aikatawa).

Godiya ta tabbata ga Allah, Ubangijin talikai, tsira da aminci su tabbata ga Manzon Allah (ﷺ) da iyalensa da sahabbansa gabaxaya.

Bayan haka, ya ku musulmai! Ku dogara kan littafin Allah, da sunnar Manzon Allah (ﷺ) wajen sanin sunayen Allah Ta’ala, saboda bai halatta ga wani ya ambaci Allah, da abin da Allah bai ambaci kansa da shi ba, ko Manzonsa bai ambace shi da shi ba. Saboda sunayen Allah Ta’ala, sai da nassi ake sanin su. Alqur’ani mai girma, cike yake da sunayen Allah Ta’ala, da siffofinsa. Misali, Allah yana cewa,

(هُوَ اللَّهُ الَّذِي لَا إِلَهَ إِلَّا هُوَ الْمَلِكُ الْقُدُّوسُ السَّلَامُ الْمُؤْمِنُ الْمُهَيْمِنُ الْعَزِيزُ الْجَبَّارُ الْمُتَكَبِّرُ سُبْحَانَ اللَّهِ عَمَّا يُشْرِكُونَ 23هُوَ اللَّهُ الْخَالِقُ الْبَارِئُ الْمُصَوِّرُ لَهُ الْأَسْمَاءُ الْحُسْنَى يُسَبِّحُ لَهُ مَا فِي السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ وَهُوَ الْعَزِيزُ الْحَكِيمُ 24)[الحشر: ٢٣ - ٢٤].

(Shi Allah, shi ne wanda babu abin bauta bisa cancanta sai shi, Masanin abin da ya vuya da abin da ya fito fili, shi ne Mai rahama, Mai jin qai. Shi Allah, babu wani abin bauta bisa cancanta sai shi, Mai sarauta, Tsarkakakke, Mai aminci, Mai kuvutarwa, Tsayayye, Mabuwayi, Mai qarfi, Mai ji da kai, tsarki ya tabbata ga Allah ga abin da suke yi na shirka. Shi Allah, shi ne Mai halitta, shi ne Mahalicci, Mai qaga halitta, Mai suranta ta, sunaye mafiya kyau sun tabbata gare shi. Abin da yake sama da qasa suna tsarkake shi, kuma shi Mabuwayi ne, gwani mai hikima).

Kuma Ubangiji ya ce,

(قُلْ هُوَ اللَّهُ أَحَدٌ1 اللَّهُ الصَّمَدُ2 لَمْ يَلِدْ وَلَمْ يُولَدْ 3 وَلَمْ يَكُنْ لَهُ كُفُوًا أَحَدٌ4)[الإخلاص: ١ – ٤].

(Allah shi kaxai ne. Allah shi ne wanda zukata suke buqatuwa zuwa gare shi, bai haifa ba, kuma ba a haife shi ba, kuma ba wani da yake kwatankwacinsa).

Ya zo cikin hadisi, “Haqiqa Allah kyakkyawa ne, yana so kyau.” [Ibni Hibban ya rawaito shi].

Kuma Manzon Allah (ﷺ) ya ce, “Lallai Ubangiji mai kunya ne, mai sitirtawa, yana son kunya da sitirtawa. idan xayanku zai yi wanka, ya vuya.” [Abu Dawud da Nasa’i suka rawaito shi].

Manzon Allah (ﷺ) ya kasance, sau da yawa, yana roqon Allah da sunayensa mafiya kyau. An karvo daga Shaddad bin Aus, daga Manzon Allah (ﷺ) ya ce, “Shugaban Istigfari shi ne, “Ya Allah! Kai ne Ubangijina, babu abin bauta bisa cancanta, sai kai. Kai ne ka halicce ni, kuma ni bawanka ne. Kuma ina bisa alqawarinka da wa’adinka, iyaka iyawata, ina komawa gare ka da ni’imarka, kuma ina komawa gare ka da zunubina, don haka, ka gafarta mini, domin babu wanda zai gafarta zunubai, sai kai. Ina nema tsari daga gare ka daga sharrin abin na aikata.” Manzon Allah (ﷺ) ya ce, “Idan bawa ya faxi wannan lokacin maraice, sai ya mutu, zai shiga aljanna, ko yana cikin ‘yan aljanna; idan ya faxa da safe, sai ya mutu a ranar, kwatankwacin haka.” Bukhari ne ya ruwaito shi.

Kuma an karvo daga Aliyyu bin Abi Xalib, ya ce, Manzon Allah (ﷺ) ya kasance, idan ya tashi zuwa sallah, sai ya yi kabbara, sannan ya ce, “Na fuskantar da fuskata ga wanda ya halicci sama da qasa, ina mai kaucewa shirka, ina musulmi, kuma ba na aikin mushirikai. Lallai sallata da yankana da rayuwata, ga Allah suke, Ubangijin talikai, ba shi da abokin tarayya. Da haka aka umarce ni, kuma ni ne farkon masu miqa wuya. Ya Ubangiji! Kai ne sarki, babu abin bautawa bisa cancanta, sai kai. Kai ne Ubangijina, kuma ni bawanka ne, na zalunci kaina, kuma na yi iqirari da laifina, don haka ka gafarta mini laifukana gabaxaya, babu mai gafarta laifuka, sai kai. Kuma ka shiryar da ni ga xabi’u mafiya kyau, babu mai shiryarwa ga xabi’u mafiya kyau, sai kai. Kuma ka kawar mini da munanansu, babu mai tafiyar da munanansu, sai kai. Na amsa kiranka, ya Ubangiji! Alheri gabaxayansa yana hannunka, ba a danganta sharri zuwa gare ka. Ni xin nan saboda kai nake, kuma zuwa gare ka zan koma. Alherinka ya yawaita, kuma ka xaukaka, ina neman gafararka, ina komawa zuwa gare ka.” Idan ya yi ruku’i, sai ya ce, “Ya Ubangiji! Gare ka na yi ruku’i, kai kaxai, kuma da kai na bayar da gaskiya, kai kaxai, kuma gare ka na miqa wuya, jina da ganina da vargona da qashina, sun rusuna gare ka.” Idan ya xago daga ruku’i, sai ya ce, “Allah ya amsa wa wanda ya gode masa. Ya Ubangijinmu! Godiya ta tabbata gare ka, cikin sama da qasa da cikin abin da yake tsakaninsu da cikin abin da ka ga dama, na daga wani abu bayan haka.” Idan kuma ya yi sujjada, sai ya ce, “Ya Ubangiji! Gare ka na yi sujjada, kai kaxai, kuma da kai na bayar da gaskiya, kai kaxai, kuma na miqa wuya gare ka, fuskata ta yi sujjada ga wanda ya halicce ta, kuma ya suranta ta, sannan ya kyautata surarta, kuma ya tsaga mata ji da gani. Alherin Allah ya yawaita, mafi kyawun masu halitta.” Idan ya yi sallama, sai ya ce, “Ya Ubangiji! Ka gafarta mini abin da na gabatar, da abin da na jinkirtar, da abin da na voye, da abin da na bayyanar, da abin da na wuce gona-da-iri, da abin da kai ne mafi sani da shi gare ni. Kai ne mai gabatarwa, kai ne mai jinkirtarwa, babu abin bautawa bisa cancanta, sai kai.” [Abu Dawud da Tirmizi suka rawaito shi].

Ya ku ‘yan uwa! A hir xinku, kuma ahir xinku, da ku ambaci Allah da abin da bai ambaci kansa da shi, ko Manzonsa bai ambace shi da shi ba. Kamar yadda wasu mutane ke yi. Wannan jingina wa Allah ne abin da bai faxa ba. Haqiqa, Allah ya yi hani a kan yin haka. Ya ce,

(قُلْ إِنَّمَا حَرَّمَ رَبِّيَ الْفَوَاحِشَ مَا ظَهَرَ مِنْهَا وَمَا بَطَنَ وَالْإِثْمَ وَالْبَغْيَ بِغَيْرِ الْحَقِّ وَأَنْ تُشْرِكُوا بِاللَّهِ مَا لَمْ يُنَزِّلْ بِهِ سُلْطَانًا وَأَنْ تَقُولُوا عَلَى اللَّهِ مَا لَا تَعْلَمُونَ33) [الأعراف: 33]

(Ka ce, “Kaxai dai, Allah ya haramta alfasha, ta fili da ta voye, da laifi, da zalunci ba tare da gaskiya ba. Kuma kada ku haxa Allah da wani, abin da Allah bai saukar da hujja da shi ba. Kuma kada ku faxi abin da ba ku sani ba ga Allah.”

Kuma Allah ya ce,

(وَلَا تَقْفُ مَا لَيْسَ لَكَ بِهِ عِلْمٌ 36)[الإسراء: ٣٦].

(Kada ka bibiyi abin da ba ka da sani a kansa).

Ya ku musulmai! Ku ji tsoron Allah, kuma ku sani cewa za ku koma gare shi, ko kusa ko nesa. Ku yi riqo da littafin Allah, da sunnar Manzon Allah (ﷺ), kuma ku roqi Allah da sunayensa da siffofinsa, domin ya yi narko na wuta ga masu yin girman kai ga hakan. Allah ya ce, “Haqiqa waxanda suke girman kai ga roqo na, da sannu za su shiga wuta, suna qasqantattu.” Kuma ku nemi sanin ma’anonin sunayen Allah, domin suna da matuqar kyau, kuma sun qunshi ma’anoni masu girma.





Tags:




Ahmad Al-ajamy