islamkingdomfaceBook islamkingdomtwitter islamkingdomyoutube islamkingdomnew


Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.

Godiya ta tabbata ga Allah, Ubangijin halittu;

Mai rahama, Mai jin ƙai;

Mai nuna Mulkin Rãnar Sakamako.

Kai muke bauta wa, kuma Kai muke neman taimakonKa.

Ka shiryar da mu ga hanya madaidaiciya.

Hanyar waɗanda Ka yi wa ni´ima, ba waɗanda aka yi wa fushi ba, kuma ba ɓatattu ba.